Zuwan Mawakiyar Gambara Nicki Minaj Kasar Saudiyya Ya Janyo Cece-Kuce


An sanar da sunan Nicki Minaj a matsayin wadda za ta gabatar da wasa a dandalin wani taron raye-raye na shekara-shekara a Saudiyya, abin da ya jawo hayaniya a ciki da wajen kasar game da yadda abin zai kasance a kasa mai “tsauri” irin Saudiyya.

Mawakiyar hip pop din ta Amurka za ta gabatar da wasan ne a bikin Jeddah World Festival ranar 18 ga watan Yuli da muke ciki.

Bayan Minaj akwai sauran sanannun mawaka kamar Steve Aoki da Liam Payne.

Wasan da za su yi yana daya daga cikin irin sauye-sauyen da Saudiyya ke samarwa game da harkar nishadantsarwa a kokarinta na habaka bangaren adabi a kasar.


Like it? Share with your friends!

-4
90 shares, -4 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like