Zulum ya ziyarci yan gudun hijirar da suka dawo Damasak daga Nijar


Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ziyarci yan gudun hijirar da suka dawo garin Damasak, hedkwatar karamar hukumar Mobbar, daga jamhuriyar Nijar.

Daruruwan yan gudun hijira ne suka dawo gidajensu dake garuruwa daban-daban a karamar hukumar ta Mobbar

Tun shekaru biyar da suka wuce ne mutanen suka tsallaka jamhuriyar Nijar sakamakon hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram kan kauyukansu.

Jumullar magidanta 674 ne suka dawo inda gwamnan ya raba musu tallafin kudi dana kayan abinci.

A yayin ziyarar gwamnan ya bada umarnin a gudanar da wasu ayyuka ciki har da gyaran wurin noman rani da kuma aikin gadar da ta haɗa garin da jamhuriyar ta Nijar.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 11

Your email address will not be published.

You may also like