Zulum ya dakatar da baki dayan ma’aikatan asibitin Ngala


Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya dakatar da baki dayan ma’aikatan babban asibitin garin Ngala dake jihar.

Ma’aikatan da aka dakatar sun hada da likita, ma’aikatan jiya,masu bada magani da kuma na dakunan gwaje-gwaje.

Gwamnan ya kai wata ziyarar bazata asibitin a safiyar ranar Litinin amma baki dayan ma’aikatan asibitin da gwamnatin jihar take biyansu albashi basa nan.

An rawaito cewa sun barwa ma’aikatan kungiyoyin agaji su cigaba da gudanar da kula da daruruwan marasa lafiya dake asibitin ciki har da waɗanda da suke sansanin yan gudun hijira.

Da isarsa gwamnan ya samu tarba daga wani jami’in tsare-tsare na wata kungiyar agaji dake asibitin.

Gwamnan ya bayyana rashin jin dadinsa kan abin da ya tarar na duk da fitowar marasa lafiya masu yawan gaske babu wani ma’aikacin gwamnati dake asibiti.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like