Zulum ya bada umarnin bincikar gobarar da ta tashi a Kasuwar Jagol


Gwamnan jihar Borno,Babagana Umara Zulum ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan gobarar da ta tashi a kasuwar yan waya ranar Alhamis da daddare.

Isa Gusau mai taimakawa gwamnan kan hulda da jama’a shine ya bayyana haka ranar Juma’a a cikin wata sanarwa da aka fitar a Maiduguri.

Gusau ya bayyana cewa Zulum ya umarci shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar,Babagana Wakil da ya binciki musabbabin tashin gobarar da kuma barnar da tayi kana ya mika rahotonsa cikin sa’o’i 24.

A ranar Alhamis ne gobara ta tashi a kasuwar waya da ake kira Kasuwar Jagol inda ta lakume shaguna da dama tare da lalata dukiya ta daruruwan miliyoyin naira.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like