Garin Kano ya yi cikar kwari yayin da dantakarar shugaban kasa Atiku Abubakar ke ziyarar yakin neman zabe.

Tituna da dama dake birnin sun shafe makil da mutane dake sanye da jar hula dake nuna biyayya ga darikar Kwankwasiya.

Dantakarar shugaban kasar da tawagarsa sun shafe sa’o’i da dama akan hanya kafin su isa fadar Sarkin Kano Muhammad Sunusi.

Daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano ya zuwa fadar sarkin tafiya ce da ba tafi mintuna 30 amma sai da tawagar ta shafe sama da sa’o’i 3 saboda da cinkoson jama’a.

Shin ko hakan na nufin karɓuwa da Atiku ya yi a Kano zabe ne kawai zai bayyana haka.