Rundunar yan sandan jihar Filato ta tabbatar da cewa wani mutum mai suna Nyam Choji dake kauyen Shen a karamar hukumar Jos ta kudu ya cinnawa yayansa wuta kan zargin maita.

Mai rikon mukamin kakakin rundunar ‘yansandan jihar,ASP Uba Gabriel wanda ya tabbatarwa jaridar Daily Trust faruwar lamarin ranar Lahadi ya bayyana suna yaran da suka hada da Godsgift Nyam mai shekaru 11 da kuma Mary Nyam mai shekaru 5.

Ya ce lamarin ya faru ne ranar Juma’a.

“Daga bayanan da muka samu mahaifin yaran da kuma ƴaƴan mai unguwar yankin sune suka aikata laifin.Yanzu haka sun cika wandonsu da iska.Amma muna saka idanu a yankin a duk tsawon sa’o’i 24 domin kama su,” ya ce.

A cewar yansandan an kai yaran asibitin kwararru na jihar Filato.