Zango Ya Tallata Wa Duniya Sabuwar Motarsa Ta Naira Miliyan 23


Shahararren dan wasan kwaikwayo a harshen Hausa, Adam A. Zango, ya tallata wa duniya sabuwar motarsa kirar ‘2019 Wrangler Jeep’ da ya siya.

Jaridar Daily Trust ta yi rahoton cewa dan wasan kwaikwayon ya sayi motar a kan naira miliyan 23.

Da yake wallafa hoton motar a kan shafinsa na Instagram a ranar Talata, Zango ya yi fariyar cewa wannan lokacinsa ne da tauraruwarsa za ta haska fiye da ta kowa.

Ya rubuta cewa: “Bayan wannan murmushin, akwai tarin godiya ga Allah a game da dukkan abubuwan da ya yi da kuma wanda zai yi a gaba. Na karbi wannan motar jif din da sunan Allah (SWT). Lokacina ne da tauraruwata za ta haska fiye da ta kowa. Ina godiya ga dukkanku a kan goya min baya a wannan lokacin.”


Like it? Share with your friends!

2
83 shares, 2 points

Comments 3

Your email address will not be published.

  1. TO MUNJI MUNGANI ALLAH YA SANYA ALKAIRI, AMMA AYI HATTARA BA FARIYABA. A MUSULINCHI ALLAH YA HANA FARIYA. KAMA KASANI ANCE IN ZAKAYI KYAUTA DA HANNUN DAMA KARKA BARI HANNUN HAGUYASANI, SAI GASHI WATARANA WAI DAN KASAYAMA MAHAIFIYARKA MOTA SAI KA TALLATAWA DUNIYA, UWA DA TAFI KARFIN MOTA AGAREKA DAN ALLAH ADINGA TUNANI KAFIN AYI DUK WANI ABU. ALLAH YA SANYA ALKAIRI AMEEEEEEEN.

You may also like