Zancen An Kore Ni Daga Jam’iyyar APC Ba Gaskiya Bane – Abdulmumin Jibril An janyo hankali na a kan wani labarin kanzon kurege na wasu maciya amanar al’umma da kokarin cin zarafi da burin tozarci gareni in da suka ce an kore ni daga Jam’iyyar APC a matakin Karamar Hukuma.

Wannan labari da muka samu wanda ya shiryashi mutum ne da yake dan cin amana da rashin dabi’a mai inganci. Wannan mutum ba shine Shugaban Jam’iyya APC ba a Karamar Hukuma Bebeji, kuma baya cikin  masu fada aji na Majalisar Shuwagabannin Jam’iyyar a matakin Jiha. A takaice ita  kanta Jam’iyya bata san da wannan batu nashi na karya ba wanda yake yadawa a kafafen yada labarai.

Wannan wani sabon matakin cin zarafi na ne daga dangin gurbatattun ‘Yan Siyasa da suka ci alwashin bata min suna da kokarin dakushe hobbasan da nake na yakin tabbatar da abubuwa bisa turbar gaskiya da rikon amana da shugabanni na gaskiya irin su Baba Buhari suke, ire iren wannan mutune sune suke ta kokarin tadiye mana kafa, mu masu kishin tabbatar da manufofi ingantattu.

In zaku tuna na amsa gayyatar da EFCC suka yi mini don karin haske akan zarge zarge da nayi akan cin hanci da rashawa wanda shuwagabannin Majalisar Tarayya sukai ta aikatawa, wanda  ni na ki bin ire iren wadannan dabi’a da ire iren masu yinta, haka itama uwar Jam’iyya ta nuna kyama ga irinsu. 

Shi mai kitsa wannan karya a gareni sune sojojin haya da wadancan mugayen mutane suka haya daga Abuja  don tabbatar da sai sunyi duk yadda zasuyi don su janye hankalina daga kwazon yaki da munanan dabi’unsu na cin hancin da kururuwar da nake tayi don dakile su.

Ina jan hankalin al’umma, mafi muhimmanci  kafafen yada labarai da cewa wannan labari bashi da asali ko tushen gaskiya daga Jam’iyyar APC. Ina da kyakkawar dangantaka da Uwar Jam’iyya ta, kuma muna nan muna ta aiki ba dare ba rana don cimma ingantattun manufofi na wannan Jam’iyya mai albarka don ciyar da kasar Najeriya gaba.
Nagode

Comments 0

Your email address will not be published.

Zancen An Kore Ni Daga Jam’iyyar APC Ba Gaskiya Bane – Abdulmumin Jibril 

log in

reset password

Back to
log in