Zan Karbi Mulki Daga Hannun Buhari…Nine Shugaban kasa Na Gaba -FayoseAyodele Fayose, gwamnan jihar Ekiti, yace yana da dukkanin abinda ake bukata domin kwace mulki daga hannun shugaban kasa Muhammad Buhari. 

Da yake magana yayin wata ganawa  da masu rike da mukaman siyasa a jihar, a gidan gwamnati dake Ado Ekiti, Fayose ya bayyana kansa a matsayin mutumin da Jama’a  suke so. 

Ya kuma kalubalanci tsofaffin gwamnonin jihar Segun Oni da kuma Kayode Fayemi,wadanda ake gani suna da Burin sake tsayawa  takarar kujerar mulkin jihar a 2018.

Yace mutane baza su basu dama ba a karo na biyu, saboda basuyi aiki  ba kamar yadda mutane sukayi tsammani. 

” Ina da matukar son karbar mulki, wanda yake hannu Buhari ma zan karba, daga na sai fadar shugaban kasa kai tsaye ,nine shugaban kasa Najeriya anan gaba kadan,”yace. 

” Ina so na zama shugaban kasar Najeriya na gaba,nawa mulkin bazai kasance irin wannan canjin ba da bai kawo komai ba, zamu wakilci al’umma sannan mu fada musu gaskiya.

“Kawai dan Ayo Fayose yaci zaben gwamna a karo na biyu,wasu mutane suna tunanin dawowa yanzu amma inaso na da fada musu ba abune mai yiwuwa ba. 

“Nine mutumin da mutanen Ekiti suke so da zuciya daya saboda aiyukan cigaba da na kawo musu. 

“Idan ka zagaya cikin Ekiti, zaka ga aiyuka na a kowanne lungu da sako na jihar nan. Saboda haka nine mutumin da dukkanin mutanen Ekiti zasu bi a shekarar 2018,”yace.  

Comments 0

Your email address will not be published.

Zan Karbi Mulki Daga Hannun Buhari…Nine Shugaban kasa Na Gaba -Fayose

log in

reset password

Back to
log in