Zan iya ficewa daga jam’iyar PDP- Fayose


Toshon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya ce zai iya ficewa daga jam’iyar PDP.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Fayose ya ce baya dana sanin goyon bayan, takarar Aminu Waziri Tambuwal.

Toshon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ne ya kayar da Tambuwal a zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.

Amma gwamnan baya dana sanin hadewa da gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike da suka yi wajen goyon bayan takarar,Aminu Waziri Tambuwal.

Wike na daga cikin na gaba-gaba dake goyon bayan Tambuwal.

“Bama dana sanin hada kai da Wike wajen goyon bayan Tambuwal a neman tikitin takarar shugaban kasa babu bukatar bayar da hakuri,” Fayose ya ce.

“Zan iya janye kasancewa ta mamba a jam’iyar idan bukatar haka ta taso amma a yanzu nida magoya bayana za mu cigaba da tattaunawa tare da duba abubuwan dake faruwa,”


Like it? Share with your friends!

-1
60 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like