Zan Bawa Yan Najeriya Mamaki Wajen Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Idan Na Zama Shugaban Kasa -Atiku


Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yace zai bawa yan Najeriya mamaki ta irin hanyar da zai yaki da cin hanci da rashawa idan aka zabe shi shugabancin kasarnan.

Atiku yace wadanda suke zarginsa da aikata cin hanci har yanzu sun gaza kawo hujja daya da zata nuna cewa zargin da suke gaskiya ne.

Yace wadanda suke zargin yayi barna da dukiyar gwamnati lokacin yana aiki to su shigar da korafi akansa a hukumar yaki da cin hanci da rashawa.

A wata sanarwa da ofishin yada labaransa ya fitar, Atiku yayi wannan maganar ne a ranar Litinin yayin bude kamfanin dab’i mai suna Yaliam, a Jabi dake Abuja.

  An rawaito shi  yana cewa ” Zan bawa kowa mamaki saboda na yarda cewa zan  yaki cin hanci da rashawa fiye da yadda aka taba yi a baya.”
“Abin takaici ne wasu mutane da suka gaza kawo sheda guda daya su cigaba da zargina da aikata cin hanci da rashawa.

 “Mutanen da basu da tunanin yadda zasu nemi kudi, a ko da yaushe tunaninsu shine kowa ma barawo ne kamarsu.

“Idan Atiku barawo ne kawai saboda dukiyarsa da kuma jarin da yake dashi a kamfanoni to makiyana a siyasa  su fito su  fadawa yan Najeriya yadda suka tara kazamar dukiyarsu.” 

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like