Zamu rika zartar da kasafin kudi cikin watanni- Ahmad Lawan


Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce daga yanzu majalisar ƙasa zata tabbatar da kasafin kudin gwamnatin tarayya cikin watanni uku bayan bangaren zartarwa ya mika masu.

Lawan ya yi wannan alƙawarin ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai dake fadar shugaban kasa,bayan da ya gabatar da sallar Juma’a tare da shugaban kasa Muhammad Buhari a masallacin dake fadar ta Aso Rocka

Amma kuma ya yi fatan cewa bangaren zartarwa za su tabbatar da mika kasafin kudin akan lokaci domin majalisun su samu damar tattaunawa a kai kafin su zartar da shi.

“Lallai wannan wani abu ne mai muhimmanci dake damun kowa da kowa, kowane dan Najeriya na son ganin majalisar kasa ta zartar da kasafin kudi akan lokaci abin da yake zuciyar mu da kuma muka yi yakin neman zabe bisa doransa, abu ne da dukkannin mu a majalisar ƙasa muka amince da shi cewa zamu zartar da kasafin kudi cikin watanni uku da izinin Allah,”ya ce.


Like it? Share with your friends!

1
79 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like