Zamu bi umarnin kotu wajen sakin Elzakzaky- DSS


Hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ta ce zata bi umarnin kotu da ya bawa shugaban kungiyar shi’a a Najeriya, Sheikh Ibrahim Elzakzaky damar zuwa kasar Indiya domin a duba lafiyarsa.

Wata babbar kotu dake Kaduna ita ce ta bayar da umarnin ranar Litinin biyo bayan bukatar da babban lauya, Femi Falana( SAN) ya shigar gabanta.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin mai magana da yawun hukumar, Peter Afunaya ya tabbatar da cewa hukumar ta karbi sakon umarnin kotun.

Ya kara da cewa hukumar na hada kai da hukumomin da suka da ce wajen ganin an tabbatar da bin umarnin bisa sharudan da kotun ta gindaya

Kotun ta bawa Elzakzaky izinin tafiya kasar Indiya a duba lafiyar sa bisa wasu sharuda da suka hada da rakiya daga jami’an hukumar ta DSS da kuma na gwamnatin jihar Kaduna.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like