A jahar da ke yankin arewacin Najeriya, ‘yan bindiga suka sace mutanen a yayin wasu jerin hare-hare da suka kaddamar a wasu kauyukan jahar. Rahotanni sun ce, sun halaka mutum guda. Wasu mazauna garin Shinkafi, karamar hukumar da ‘yan bindiga suka yi wa dirar mikiya, sun sheda ma kamfanin labaran Reuters cewa, maharan sun kai saba’in da suka goyo juna kan babura, inda suka yi ta harbe-harbe da banka wa gidaje da shaguna wuta.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, ya sheda ganin yadda maharan suka harba wani roka kan gidan mai garin yankin. Babu wani cikakken bayani daga mahukuntan jahar kan wadannan hare-haren tukun na. Lamarin na daren Juma’ar da ta gabata, ya haifar da rudani inda ya tilasta ma jama’ar garuruwan tsere wa daga gidajensu.