Gwamnatin Nijar ta bayar da umarnin sauko da tutar kasa a duk sassan kasar a yayin da ta sha alwashin ci gaba da yakar ayyukan ta’addanci har sai ta kai ga cimma nasara.

Yankin da aka kai harin dama na fama da ayyukan mayakan Al-Qaeda da IS, sai dai kuma harin na kauyen Dare-Day da ke jahar Tillabery, ya tayar da hankula da jefa jama’a cikin fargaba, ganin yadda maharan da suka kai hari kan manoma, a wannan karon suka hada da mata da kuma kananan yara. 

A wani rahoto da Kungiyar Human Rights Watch ta fitar a makon jiya, ta ce, fararen hula sama da 420 ne suka rasa rayukansu a sakamakon hare-haren mayakan da ke da’awar jihadi a jahar ta Tillabery.