Zakzaky ya shilla kasar Indiya Da misalin Karfe 6 Na Yamma


Da misalin 6:00pm na yammacin yau litinin Shugaban kungiyar IMN wanda akafi sani da Shi’a, Sheik Ibrahim El-Zakzaky, ya tashi zuwa kasar Indiya a filin jirgin sama na Nmandi Azikwe a jirgin Emirites domin jinya biyo bayan belin da kotun jihar Kaduna ta bashi a makon da ya gabata.

A baya Mun kawo muku rahoton cewa an tafi da Sheik Ibrahim Zakzaky birnin tarayya Abuja.

El-Zakzaky ya tafi Indiya tare da matarsa Zeenat inda za su nufi Asibitin Medenta dake New Delhi a kasar ta Indiya domin a duba lafiyarsu.


Like it? Share with your friends!

-2

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like