Zainab Aliyu ta dawo gida Najeriya bayan watanni hudu tana tsare a kasar Saudiyya


Zainab Aliyu, yar Najeriya da kwanakin baya aka tsare a kasar Saudiyya bayan da aka zarge ta da safarar miyagun kwayoyi ta dawo gida bayan da ta shafe watanni hudu a tsare a hannun hukumomin Saudiyya.

An kama Zainab ne cikin watan Disamba a birnin Madina bayan da aka samu wata jaka dake dauke da sunanta wanda aka saka ƙwayar Tramadol.

Bayan da mahaifinta ya shigar da korafi hukumomi sun tashi tsaye anan gida Najeriya dama can kasar Saudiyya har ta kai ga an kama wasu mutane a filin jirgin saman Kano wadand ke da hannu a jefa Zainab cikin mawuyacin hali.inda aka tabbatar da cewa bata da laifi

Ta iso Najeriya ta filin jirgin saman Malam Aminu Kano tare da wani dan Najeriya mai suna Ibrahim Abubakar da aka kama shi da irin laifin da ake zarginta da aikatawa.

Zainab mai shekaru 22 wacce daliba ce a jami’ar Maitama Sule dake Kano taje kasar Saudiyya ne domin yin aikin Umrah tare da mahaifiyarta da kuma yaruwarta.


Like it? Share with your friends!

-2
97 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like