Zainab Aliyu Da Aka Yi Wa Cushen Kwaya A Saudiyya Ta Dawo Nijeriya


Yarinya ‘yar makaranta wacce aka makalawa kwaya a filin sauka da tashin jirage dake Kano, wacce jami’an tsaron kasar Saudia suka kwamushe ta, bayan da ta sauka a kasarsu tare da muggan kwayoyin daba nata ba.

Yarinyar da ake shirin saka ta a layin wadanda za a datsewa kawuna a can kasar ta Saudia….

Ita dai yarinyar da ‘yan Arewa suka samu hadin kan da suka dade basu samu irinsa ba, wajen nemar mata kubuta daga hukuncin laifin da bata aikata ba, har aka samu nasarar kubutar da wuyan ta daga wukar hauni.

Yanzu dai yarinyar ta dawo Nijeriya a wannan rana ta Litinin, inda dai ta sake sauka a filin jirgin malam Aminu Kano dake Kano yarinya Zainab Aliyu kenan.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like