Ana zaben lokacin da ake ci gaba da fuskantar annobar cutar coronavirus wadda ta halaka fiye da mutane 180,000 a kasar tare da jefa wasu milyoyin mutane cikin kangin talauci.

An yi zagaye na farko na zaben kasar ta Peru da ke yankin kudancin Amirka a watan Afrilu inda ‘yan takaran biyu suka fi samun kuri’u kuma wannan zaben zai tantance wanda zai jagoranci kasar na gaba tsakanin Pedro Castillo dan shekaru 51 da haihuwa malamin makaranta da Keiko Fujimori ‘yar shekaru 46 da haihuwa.