Zaben Shugaban Majalisar Dattawa: Ahmad Lawan Ya Samu Nasara A Kan Ndume


Sanata Ahmad Lawan na jihar Yobe ya samu nasarar zamowa shugaban majalisar dattijai ta tara bayan ya kayar da abokin karawarsa, Sanata Ali Ndume na jihar Borno.

Ahmad Lawan ya samu kuri’u 79 a cikin 107, yayin da Ali Ndume ya samu 28.

Bayan kammala zaben, magatakardar majalisar, Muhammad Sani-Omolori, ya bayyana sunan Ahmad Lawan a matsayin wanda ya samu nasara.

Bayan nan Sani-Omolori ya bayyana cewa sanatoci 107 ne suka kada kuri’ar.


Like it? Share with your friends!

-1
89 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

  1. naji dadin hakan wallahi.
    ndume sanatanmune amma ni banga anfaninshi ba.domin bai damu da halinda yan gudun hijira suke cikiba musamman yan gudun hijiran PULKA akalla akwai yan gudun hijira fiyada dubu hamsin amma ndume bai taba ziyartarsu ba.kuma tahanyan yana wucewa gwoza.dan haka bana bakin cikin rashin nasararsa dominshi bishiyan giginya ne.

You may also like