Zaben gwamoni: Akwai ayar tambaya a kan gaskiyar Buhari – Aliyu Sani Madaki


Dan majalisar wakilai na tarayya daga jihar Kano Aliyu Madaki ya ce akwai ayar tambaya a kan gaskiyar Shugaba Muhammadu Buhari duba da yadda aka ki kammala zabukkan gwamnoni a wasu jihohi na Najeriya.

Madaki ya ce ya kamata a sake bibiyar gaskiyar shugaban kasar duba da yadda ya yi gum da bakinsa akan yadda aka gudanar da zabuka a wasu jihohin Najeriya.

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Dala a jihar Kano ya fadi hakan ne yayin da ya ke tofa albarkacin bakinsa kan wani kudiri da wani dan majalisa ya gabatar ranar Laraba.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta ce zabuka ba su kammala ba a jihohi shida a Najeriya bayan soke sakamakon zabukkan wasu mazabu a jihohin.

Daga bisani hukumar zaben ta zabi ranar 23 ga watan Maris a matsayin ranara da za a sake maimaita zabukan a jihohin Benue, Sokoto, Plateau, Adamawa, Kano da Bauchi.

A jawabinsa, Madaki na jam’iyyar PDP ya zargi Shugaba Muhammadu Buhari da kawar da kansa dangane da wasu abubuwan da ba saba gani ba da INEC keyi.

Yace “Idan shugaban kasa yana da sauran gaskiya, ya kamata a sake bibiyar wannan gaskiyar. Ba zamu amince ba, ba zamu bari ta faru ba. Ba za ta faru ba.”

Ya ce duk da cewa ba zaiyi magudin zabe ko ya goyi bayan hakan ba, “babu wanda zai yi mana magudi” a Kano. “Babu wanda zai zo Kano ya tilasta mana. Kano ba Legas bace,” inji shi.

A yayin da ya ke jawabinsa, Muhammad Soba daga jihar Kaduna ya ce INEC ba ta da ikon cewa zabe bai kammala ba bayan an gama kirga kuri’u.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like