Zaben cike gurbin Katsina: PDP ta samu kuri’a 1 a mazabar Buhari


Kabir Babba Kaita, dantakarar jam’iyar PDP a zaɓen cike gurbin sanata mai wakiltar mazabar arewacin Katsina ya samu kuri’a daya cal a mazabar ‘Sarkin Yara, A’ dake karamar hukumar Daura ta jihar Katsina

Shugaban kasa Muhammad Buhari na kada kuri’arsa ne mazabar

Ahmad Babba Kaita dantakarar jam’iyar PDP ya samu kuri’a 266.

Har ya zuwa yanzu ana cigaba da tattara sakamako a zaben.

Hukumar Zabe ta kasa INEC na gudanar da zaɓen cike gurbin biyo bayan mutuwar sanata Mustapha Bukar dake wakiltar mazabar cikin watan Afrilu.


Like it? Share with your friends!

2
142 shares, 2 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like