ZABEN CIKE GURBI NA YAN MAJALISU A KANO: APC TA LASHE KUJERU 5 YAYIN DA PDP TA LASHE KUJERA 1


Ayayin zaben cike gurbi da aka gudanar ajahar kano A kananan hukumomin Mnijibir, Madobi, Rogo na yan majalisun jaha. Sai kananan hukomomin Komboto, Tudunwada/Doguwa,Kiru/Bebeji.

Hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa ta bayyana sakamakon Kamar haka
Tudun wada dogowa Dan takarar APC Hon Alhassan ado doguwa yasamu kuri’u 66,685
Sai yusha’u soja na Jamiyyar PDP Ya samu kuri’a 6323.

Sai kuma sakamakon Kiru/Bebeji hukumar zabe ta bayyana Hon Ali datti yako na jamiyyar PDP A matsayin wanda ya lashe zaben
A Karamar hukumar kombotso hukumar zaben ta bayyana hon Muneer babba Dan agundi na jamiyyar Apc amatsayin wanda ya lashe zaben na dan majalisar tarayya.

Sai sakamakon Yan majalisun jaha
Hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyan Hon tasi’u zabainawa Amatsayin wanda yalashe zaben dan majalisar jahar Akaramar hukumar minjibir Yayin Hon ismail muhammad chinkoso ya lashe zaben dan majalisar jahar madobi A jamiyyar APC.

Sai karamar hukumar Rogo inda hukumar zabe ta bayyana hon magaji zarewa na jamiyyar Apc amatsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar jahar kano akaramar hukumar Rogo
Wadanan sune sakamakon cike gurbe da aka gudanar a ranar asabar 25/1/2020 A jahar Kano.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like