Wasu matasa ‘yan Jam’iyyar PDP dake goyan bayan Alhaji Atiku Abubakar, ya tsaya takarar neman shugabancin Nigeria a shekarar 2023, sun kirkiro wata babbar sabuwar kungiya mai karfi a yankin Arewa maso gabas domin tallafawa tafiyar.

Jajirtattun matasan sun sakawa kungiyar suna “NORTHEAST YOUTH SUPPORT ATIKU FOR PRESIDENT 2023”.Matasan sun kirkiro wannan kungiyar ne, domin kishin wannan yanki nasu da kuma ganin dan wannan yanki nasu yayi shugabancin kasar Nigeria a mulkin farar hula.

Idan baku manta ba, tun bayan marigayi Abubakar Tabawa Balewa da yayi mulkin kasar daga yankin, babu wanda ya sake mulkin kasar daga yankin.

Da wannan dalilin ne kungiyar take kira ga Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa da ya fito ya cire musu kitse a wuta inji mabiya kungiyar.

Haka zalika kungiyar bata tsaya anan ba, tana tallafawa marassa karfi, nakasassu, marayu, yan gudun hijira, da duk wasu al’ummar da suke cikin wani hali na taimako.

Kungiyar ta nada rassa da dumbin mabiya a dukkanin Jihohin yankin Arewa maso gabas da suka hada da Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Yobe, Taraba.

Dukkan wannan hidima da wannan kungiya take yiwa talakawa da marassa karfi karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa kuma wanda ya assasa kungiyar Comr. Sadiq Musa Gomari, haifaffan dan jihar Borno dake zaune a garin Adamawa.

A karshe Kungiyar tana Kira ga dukkanin al’ummar wannan yanki da suzo ayi wannan tafi dasu domin tafiyar ta kowa da kowace, kungiyar tana maraba da dukkanin wanda zaizo ya bada tashi gudummuwar ga yankin.