ZABEN 2023: Magoya Bayan Buhari Na Son Jonathan Ya Dawo Mulki


Gabannin zaben shugaban kasa na 2023, an rahoto cewa magoya bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari na duba yiwuwar marawa tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan baya don darewa kujera mafi muhimmanci a kasar.

Jaridar This Day ta ruwaito cewa wannan tunanin shine cewa hakan zai kwantar da hankalin masu matsa lamba don ganin mulki ya koma yankin kudu.

A cewar rahoton, makusantan Buhari na ganin cewa Jonathan ne mutumin da ya fi dacewa da wannan matsayin idan har za a mika shugabancin kasar ga yankin kudu.

Wata babbar majiya a sansanin Buhari wacce bata so a bayyana sunanta, ta ce:

“Ya mika mulki cikin lumana sannan bai kullaci kowa da mugun nufi ba saboda haka ba zai zama barazana ga ra’ayin arewa ba.”

Wani dalili da yasa wadannan masu biyayya ga Buhari ke duba yiwuwar marawa shugabancin Jonathan baya a 2023 shine cewa zai yi mulki ne na zango daya.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like