ZABEN 2023: Ba Za Mu Sake Yarda Da ‘Inconclusive’ a Jihar Kano ba – Sanata Kwankwaso


Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya gargadi jam’iyyar APC a jihar cewa PDP ba za ta sake amincewa a maimaita mata ‘inconclusive’ kamar yadda aka yi a zaben shekarar 2019 ba.

Sanata Kwankwaso ya ce shi da jam’iyyarsa na PDP da magoya bayansa ‘yan Kwakwasiyya, ba za su amince a sake maimaita hakan ba.

A 2019, PDP na kan gaba a zaben gwamna a Kano kafin hukumar zabe, INEC, ta ce zaben bai kammalu ba.

Daga bisani aka yi zaben raba gardama a wasu yankuna kuma APC ta yi nasara, hakan ya bawa gwamna Abdulllahi Ganduje nasarar zarcewa kan mulki.

Kwankwaso ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis, yayin da ya ke yi wa magoya bayansa jawabi inda suka rika jinjina masa.

Daga bisani an wallafa bidiyon jawabin a shafin Facebook na Kwankwasiyya da aka saba wallafa labaran siyasa masu alaka da jigon na PDP.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like