Za’ayi Duk Wacce Za’ayi Muddin Aka Sake Akai Magudi A Zaben 2019 – Orubebe


Tsohon ministan harkokin Niger Delta, Godsday Orubebe ya caccaki yadda aka gudanar da zaben 2015 sannan ya sha alwashin cewa ba za’a bari a yi magudi a zaben 2019 ba.

Orubebe wanda ya kasance dan jam’iyyar PDP, ya tada wata rigima a lokacn hada sakamakon zaben shugaban kasa na 2015 lokacin da yayi zargi cewa shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na waccan lokacin, Farfesa Attahiru Jega ya nuna son kai a hada sakamakon, harma Orubeben yayi yunkurin hargitsa shirin.

Tsohon ministan, ya fadawa mujallar TELL cewa ba za’a bari ayi magudin zabe kamar yadda aka yi a Ekiti da Osun ba a 2019.

A cewarsa, babu wanda ya isa ya takewa yan Najeriya hakkinsu na zabar shugaban kasar su a 2019.


Like it? Share with your friends!

-1
146 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

  1. to allah yakaimu, aigaskiya ztayi halinta a 2019 din. Yadda mukayimu a 2015 ma sai yafi wannan wahala da yardar allah.

You may also like