ZA’A BUDE KATAFAREN GIDAN MAI MAFI GIRMA A AREWACIN NAJERIYA A GARIN TAMBURAWA TA JIHAR KANO


Turkashi, lallai Malam Bahaushe yayi gaskiya da yace wai “mai kamar zuwa kan aika.”

Wannan batu haka yake la’akari da yadda shahararren kamfanin na Salbas Oil and Gas, mallakin hamshakin matashin dan kasuwa, Alh. Saleh Baba Rano, wanda ya dade da yin fice a fannin hada-hadar man fetur da dangogin sa a wannan kasa, yayi tanadin Aljannar Duniya ga abokan huldarsa ta hanyar samar da katafaren Gidan Mai, irin sa na farko a arewacin Najeriya mai lakabin komi da ruwanka. Domin kamar yadda zaku iya gani a hotunan dake kasa, wannan katafaren Gidan Mai dake garin Tamburawa kan hanyar zuwa Zaria kilomita biyar daga babban Birnin Kano, ya tanadi abubuwa more rayuwa domin jin dadin direbobi da matafiya, wadanda suka hadar da bandakunan wanka dana bahaya sama da dari kuma kyauta, sai kuma dakunan cin abinci da kayan makulashe masu tsafta, shagunan aski don manyan mutane da masu karamin karfi, shagon sayarda magunguna na zamani, nau’o’in lemuka na zamani, na’u’rori masu kwalkwalwa domin ziyartar yanar gizo a kowanne lokaci, kayan masarufi domin iyali da sauran ababen more rayuwa duk a cikin rahusa.

Akwai kuma masallaci don masallata, wadattatun filayen ajiye motocin matafiya tare da ingantaccen tsaro ga rayuka da dukiyar abokan hulda.

Hakika wannan babbar dama ce ga direbobi da matafiya, musamman wadanda suka fito daga jihohin Kano, Katsina, Zamfara da daukacin jihohin arewa maso gabas (Adamawa, Gombe, Bauchi, Taraba, Borno da Yobe), dake kan hanyar su ta zuwa Babban Birnin Tarayya Abuja ko jihohin nan 17 dake kudancin wannan kasa.

Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR, ne da kansa ba sako ba zai bude wannan katafaren Gidan Mai ranar Alhamis 29 ga watan Ogusta na 2019.

Abinda ya rage kawai a yanzu shine ni da kai mu zamo cikin sahun abokan hulda, kada ku sake a baku labari.

Wannan sakon taya murna ne ga daukacin mutanen Rano dama Jihar Kano baki daya.


Like it? Share with your friends!

-1
110 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like