A yanzu haka yaran sun kwashe kimanin kwana 23 a hannun wadannan ‘yan bindiga ba tare da samun nasarar kubutar da su ba,

Gwamnan jihar Nejan Alhaji Abubakar Sani Bello wanda ya je garin Kagara domin jajantawa iyayen daliban Islamiyyar da kuma kaddamar da wasu jami’an tsaro na musamman a ranar Litinin, ya ce akasarin masu aikata ta’addacin nan fa ba yan Najeriya ba ne, saboda haka bai kamata a saurara masu ba.

Sai dai shugaban makarantar Islamiyyar Malam Abubakar Garba Alhassan ya ce suna da fargaba ga matakin Gwamnati na neman kwato yaran da karfin bindiga saboda gudun salwantar da rayukkansu.

‘Yan Bindiga

‘Yan Bindiga

A halin da ake ciki, shugaban makarantar Islamiyyar ya ce 3 daga cikin malaman dake hannun ‘yan bindigar sun samu nasarar kubutowa.

A wani labarin kuma Gwamnatin Jihar Nejan ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan ‘yan banga kusan talatin da ‘yan bindiga suka kashe a karshen makon nan.

Gwamnan jihar Nejan ya ce lamarin abin takaici ne kuma za su tallafawa iyalansu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari: