Za Mu Kori Duk Ma’aikacin Da Muka Kama Yana Karbar Cin Hanci A Wajen Yi Wa Mutane Katin Zama Dan Kasa – Sheikh Pantami


Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, FNCS, FBCS, FIIM, ya bayar da umarnin a dakatar da duk wani ma’aikacin da aka samu da karbar cin hanci, a wajan mutanen da suke son su mallaki katin zama dan kasa nan take.

Ministan yace; ana samun wasu gura-gurbin ma’aikatan Hukumar samar da katin shaidar zama dan kasa (NIMC) a Jihohin Bauchi da Kaduna suna karbar cin hanci a hannun mutanen da suke neman katin zama dan kasa.

Ministan ya umarci hukumar NIMC reshen dukkannin Jihohi da ta samar da lambobin waya da email address wanda mutane zasu rika tura sakunan korafe-korafe zuwa ga Ma’aiktar.

Idan baku manta ba, tun a shekarar da ta gabata ministan sadarwa sheikh Pantami ya bada umurni ga dukkanin al’ummar kasar da su hada layukansu da katin dan kasarsu don tsaftace Dukkanin layukan al’ummar kasar.

Za’a rufe dukkannin layin da ba’a hadashi da katin dan kasa ba, da zaran lokacin da aka bayar ya kare, ta yadda za’a dinga gane duk wani layi da ‘yan ta’adda ke amfani dashi a fadin kasar.

Haka zalika ministan ya bawa Kamfanukan sadarwa na layuka damar fara yiwa al’ummar kasar ragistar zama ‘yan kasa ga wa ‘yanda basu da katin domin a saukaka musu.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like