A ranar Juma’a hukumomin kasar suka dakatar da amfanin da shafin na sada zumunta, bayan da suka yi zargin cewa ana yawan amfani da shi wajen gudanar da wasu ayyukan da ka iya yin barazana ga zaman lafiyar Najeriya.

Malami ya bada umarnin ne a wata sanarwa da ya fitar dauke da sa hannun mai taimaka masa a fannin hulda da jama’a Dr. Umar Jibrilu Gwandu.

“Malami ya bada umarni ga darektan hukunta laifuka na kasa da ke karkashin ofishin Atoni janar, da ya fara daukan matakan gurfanar da wadanda suka keta dokar da gwamnatin tarayya ta saka ta dakatar da Twitter a kasar.”

Sanarwar ta kara da cewa, babban atoni janar din ya ba ofishin umarni, da ya hada kai da ma’aikatar sadarwa da bunkasa tattalin arziki ta yanar gizo, da hukumar dake kula da kamfanonin sadarawa “don gaggauta tuhumar wadanda suka keta wannan doka.”

Wannan takaddama ta samo asali ne bayan da kamfanin Twitter ya goge wani sakon da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya wallafa a ranar Laraba.

Sakon ya yi gargadi ne ga kungiyar IPOB da ake zargi da ta da kayar baya a kudu maso gabashin kasar, inda ya yi masu nuni da irin asarar rayukan da aka yi a yakin basasan da Najeriya ta fuskanta.

A cikin sakon, Buhari ya yi ikirarin cewa, gwamnatin Najeriya, za ta tafiyar da masu kai hare-hare a yankin da abin da ya kamace su, kalaman da wasu ke nuni da cewa, barazana ce ga mazauna yankin wanda ya fuskanci yakin Biafra, abinda ya yi sanadin asarar rayukan ‘yan Najeriya da dama.

Twitter ya yi maza ya goge sakon Buharin, wanda ya ce ya saba ka’idojin kamfamin.

Bisa ka’ida, kamfanin na Twitter ba ya yarda a wallafa wani sako da zai iya ta da hankali ko barazana ga wani ko wasu ba.

Sai dai hukumomin Najeriyar sun zargi kamfanin na Twitter da nuna alamun goyon bayan ga fafutukar IPOB mai neman kafa kasar Biafra, suna masu cewa shugaban kungiyar Nnamdi Kanu da mambobinta, na wallafa bayanai da suka fi na Buhari a shafin na Twitter, ba tare da an dauki mataki akansu ba.

A shekarar 2017, Najeriya ta ayyana kungiyar ta IPOB a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda inda ta haramta duk wasu ayyukanta.

A lokuta da dama kungiyar ta sha nesanta kanta da hare-haren da ake zarginta d