Za Mu Hada Hannu Da Sashen Shari’a Domin Tabbatar Da Gaskiya Da Adalci A Kano – Ganduje


A yunƙurin tafiyar da al’amuran shari’a cikin sauri da managarciyar nasara kamar yadda tsarin harkokin shari’a ya ke tafiya a zamanance yau a Duniya, sashen shari’a na Jihar Kano zai fara amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa {Computer} a kotun ɗaukaka ƙara {Shari’a Court Of Appeal} domin adana bayanai da kuma tafiya da zamani.

Tun a lokacin da ya zama sabon zababben gwamnan Jihar Kano a shekarar {2015}, gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya yi alƙawarin ba wa fannin shari’a muhimmanci domin tabbatar da an gudanar da shari’u cikin tsari da nasara.

A tare da haka, gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya kafa wani kwamiti mai ƙarfi kan samar da afuwa ga ɗaurarru tun a farkon zangon mulkinsa na farko. Kuma ya samu nasarar sakin kimanin ɗaurarru (2,717) a ƴan shekarun da su ka gabata. A wani mataki na rage matsalar da aka hango ta cinkoso a gidajen gyaran hali da ɗabi’u, “Correctional Centres”, inda aka fi sani da {Prisons} na Jihar Kano.

Sabon Alƙalin-Alƙalai na Jihar Kano, Onarabul, Tijjani Yusuf Yakasai, shi ne ya ba da tabbacin fara aiwatar da sabon tsarin na fara shigarwa da kuma adana bayanai cikin na’ura mai ƙwaƙwalwa {Computer}, a jiya Juma’a, lokacin da ya ke shan rantsuwar kama aiki a matsayin cikakken alƙalin-alƙalai na Jihar Kano, a ɗakin taro mai suna {Africa House} da ke cikin gidan gwamnatin Jihar Kano.

Da ya ke yabawa mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan irin haɗin-kai da goyon bayan da ya ke ba wa fannin shari’a, alƙalin-alƙalan na Jihar Kano, Onarabul Yakasai, ya ƙara da cewa: “sabon tsarin adana bayanai a na’ura mai ƙwaƙwalwa rukuni-rukuni ne, yanzu haka rukuni na farko ya yi nisa.

A ƙarƙashin rukunin farko, akwai tsarin raba kuɗaɗen gudanarwa ga kotuna ta hanyar zamani wato {E-payment}. Sai kuma kashi na biyu na adana bayanai cikin tafiya da zamani a kotuna. Shi ma tuni ya kankama. Domin adana dukkan muhimman bayanai da takardu saboda gujewa yin asarar su. Sannan kuma Khadi ya ba da tabbacin cigaba da samar da ƙarin horo da dabarun sanin makamar aiki ga sauran ma’aikatan kotuna da alƙalai nan gaba kaɗan.

Sannan kuma Khadi ya ƙara ba da tabbacin cigaba da ɗabbaƙa sabbin tsare-tsare a kotunan ɗaukaka ƙara na Jihar Kano, domin tabbatar da tafiya da zamani kamar yadda cigaban duniya ya ke tafe kan hakan a yau tare da yunkurin zuwa mataki nagaba {NextLevel}.

Ya yin da ya ke gabatar da nasa jawabin, gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya taya Khadin murna kan yadda ya samu nasarar hayewa dukkan wasu gwaje-gwajen lafiya da na ilimi da aka yi masa.

Daga ƙarshe kuma, gwamna Ganduje ya sake yabawa da nagarta gami da ƙwazon Khadin, sannan kuma gwamna Ganduje ya ƙarƙare da ba da tabbacin samun nasarar shari’u masu aminci da nagarta a fannin shari’ar da ya kunshi mutane masu nagarta irin Khadi Yakasai.

“Mu na alfahari da kai, za mu cigaba da haɗa hannu da fannin shari’a wajen tabbatar da gaskiya da adalci a wannan fanni na shari’a. Inji Gwamna Ganduje.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like