ZA MU BA WA BUHARI KURI’U MILIYAN BIYAR -Manoman Masara


Kungiyar manoman masara ta Nijeriya, MAAN, ta bayyana cewar za ta harhada kan mambobinta masu rijista su miliyan biyar domin su zabi Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben da za a kada a ranar Asabar ta sama.

Da yake magana dazu a wani taron manema labarai da aka gabatar a Abuja, Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Bello Abubakar ya ce kungiyar ta samu matukar ci gaba a karkashin wannan gwamnatin, inda ya kara da fadin cewa Shugaban kasar ya cancanci ya zarce.


Like it? Share with your friends!

1
75 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like