Za a yi wa yan majalisar dokokin jiharKaduna gwajin cutar Korona


An umarci dukkanin yan majalisar dokokin jihar Kaduna da su mika kansu domin a yi musu gwajin cutar Korona.

Haka suma dukkanin sauran ma’aikata dake aiki a majalisar an umarce su da a yi musu gwajin na cutar Korona.

Shugaban majalisar, Yusuf Zailani shine ya bayar da umarnin bayan da aka gano wasu ma’aikatan majalisar na dauke da cutar Korona.

Ali Kalat, mataimakin shugaban kwamitin lafiya na majalisar shi ne ya sanar da haka lokacin da yake ganawa da manema labarai.

A cewarsa umarnin ya zama dole domin tantance lafiyar ma’aikata da kuma yan majalisar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like