Za a rika sayar da litar mai ₦125


Gwamnatin tarayya ta amince da rage farashin kudin litar man fetur daga ₦145 zuwa #125.

Rage farashin litar man ya biyo bayan bijiro da batun rage kudin man da karamin ministan mai Timipre Sylva ya yi a yayin zaman majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban kasa Muhammad Buhari ya jagoranta.

An amince da sabon farashin ne sakamakon faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya daga $60 ya zuwa $29.

Ana ganin cewa daga yanzu gwamnatin tarayya zata kyale farashin danyen mai a kasuwar duniya ya zama ma’aunin kudin da za a rika sayar da man fetur a cikin gida Najeriya.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 20

Your email address will not be published.

You may also like