Kafatanin kasashen sun kuduri aniyar amfani da wani kundi mai feji goma sha takwas da ya shata yadda za a rage yawan masu kamuwa da cutar daga mutane dubu 370 ya zuwa kasa da dubu 250 a shekaru hudu masu zuwa. Taron har wa yau ya bukaci kasashen da su yi mai yiyyuwa wajen rage tsangwamar da ake nuna wa masu dauke da cutar.

Zauren ya koka dangane karancin tallafi daga daidaikun al’umma da kungiyoyi masu hannu da shuni a fadin duniya, duba da bukatar da ke da akwai a kasa na ganin an samar da rigakafin cutar cikin gaggawa.