Bukatar hakan ta biyo bayan wani harin da aka kai wa dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar, makwanni uku da suka gabata a lardin Gao da ke arewa maso gabacin Mali, wanda ya yi sanadiya hallaka sojojin gwamnati goma sha biyu wasu goma sha uku suka ji mummunan rauni da suka hada da sojojin Jamus goma sha biyu da na Baljiyan guda daya rak.

Kimanin karin dakarun wanzar da zaman lafiyar 2,069 ne, ake sa ran aike wa a yankin da suka hada da dakarun soji 1,730 da na ‘yan sanda dari uku da wani abu.