Za a kaddamar da shirin rabawa matan karkara kuɗi a jihar Katsina


Ministar ma’aikatan jinkai da walwalar jama’a, Hajiya Sadiya Umar Faruq ta isa jihar Katsina a kokarin da take na kaddamar da shirin rabawa matan karkara kudi kai tsaye daga gwamnatin tarayya.

Sabon shirin zai mayar da hankali ne akan bayar da tallafi ga wasu rukunin matan karkara.

Mai taimakawa ministar kan kafafen sadarwar zamani, Nneka Ikem Anibeze ita ce ta sanar da isar ministar Katsina cikin wani sako da ta wallafa a Facebook.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like