Ko da yake shugaban na Faransa ya ce za su janye daga aikin na yaki da ta’addanci a cikin rundunar, amma ya ce sojojin su za su ci gaba da aiki a cikin rundunar soji ta hadin gwiwa tsakanin Turai da kasashen Afirka Takuba domin yakin da ta’addanci. Faransa na da sojoji sama da dubu biyar a cikin rundunar ta Barkhane ada aka kafa tun a shekara ta 2014 wacce ta yi nasara kwato yankin arewacin Mali da kungiyar ‘yan ta’adda ta Abzinawa ta kwaci iko da shi tun 2012. Fransa ta yanke shawarar dakatar da ayyukan sojojin ta ne a Mali bayan juyin mulki da sojojin suka yi na kiffar da gwamnatin wucin gadi ta farar hula a makonnin da suka gabata.