ZA A GUDANAR DA ADDU’AR SAMUN ZAMAN LAFIYA A BABBAN MASALLACIN ABUJA


A madadin maulanmu Shehu Dahiru Usman Bauchi tare da daukacin ‘yan darikar Yijjaniyya suna gayyatar al’ummar Musulunci zuwa wurin gabatar da zikirin Juma’a da yi wa kasa addu’a don samun zaman lafiya da karuwar arziki.

Za a gabatar da taron ne a babban masallacin Juma’a dake Abuja wanda aka saba gabatarwa duk shekara a farkon watan musulunci inda dubban mutane daga sassan kasar nan ke halartar taron.

Wanda zai kasance karkashin jagorancin babban malamin addinin Musulunci nan wato Sheikh Dahiru Usman Bauchi (Allah ya yarda da shi).

Za’a gabatar da taron zikirin Juma’an da zaman lafiya a gobe Juma’a 27/09/2019 a babban masallacin Juma’a dake Abuja.

Allah Ya Sa A yi Lafiya, Allah Ya Bada Zaman Lafiya A kasar Mu Nijeriya. Amin.


Like it? Share with your friends!

1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like