ZA A FARA FARAUTAR MASU YADA LABARAN KARYA


Idan jununka rubutun cin zarafin wani ko haddasa fitina ko yada labaran karya da kanzon kurege, to ina maka albishir da cewar kwanakinka na daf da karewa.

Kada wata ayar doka ta rude ka na cewar wai kowa na da ‘yancin fadin albarkacin bakinsa. Kada kirkiro akwatunan karya su rude ka a kafar sada zumunta ka yi tsammanin ba a san inda kake ba. Kada yawan abokai mazuga su rude ka zama kamar indararo wajen zuba babu kwaba.

An samu karin ci-gaba sosai wajen gano lalatattun mutane masu kunna wutar gaba da kirkiro labarun karya. Dabaru da dama wajen gano mutane….sai dai da yake lamarin ya shafi tsaro da hukuma, ba zan fade su anan ba. Sai dai kuma a rika sara ana duban bakin gatari. Duk abin da kake kattabawa a idanunmu yake. Aha!

Kafin na tafi, bari na yi talla. Kamfani mai suna Verify Me, hadaka ce ta kwararru. Aikinsu ya hada da binciken kwakkwafi ta intanet da wajen intanet wajen bincike akan mutum da tarihinsa na ciki da na boye. Aikin wannan kamfani ya hada binciko tushen labari da wanda yada shi a duniyar gizo. Da kuma binciko tarihin aikin mutum a wajen duniyar gizo da abokan aikinsa da ma’aikatarsa da sauran abokan huldarsa. Haka kuma kamfanin na iya bin diddigin ingancin wata takarda kamar ta makaranta ko ta fili da sauransu.

Ga mai son karin bayani, sai ya garzaya adireshin kamfanin a https://verifyme.ng ko a kira lambar waya, +2349060007624 ko kuwa a leka babban ofishinsu da ke 6 Furo Ezimora Street Lekki Phase 1, Lagos.

Nan gaba kadan za su bude rassa a dukkan fadin kasar nan.


Like it? Share with your friends!

1
62 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like