
Gwamnatin tarayya ta ce yan Najeriya za su samu allurar rigakafin cutar Korona a cikin watan Janairun shekarar 2021.
Ya ce wani kwamitin masana kwararru a a ma’aikatar yana aiki tukuru domin ganin wace allurar ce tafi dacewa da Najeriya duba da cewa bamu na’urorin sanyi da ake iya ajiye abu a ma’aunin sanyi na -80C.
Ministan lafiya, Osagie Ehanire shi ne ya bayyana haka a karshen taron majalisar zartarwar ta tarayya a ranar Laraba.
Tun da farko gwamnatin tarayya ta ce tana aikin tukuru wajen ganin an samue allurare rigakafin miliyan 20 a farkon shekarar 2021.
Comments 21