Za a cigaba da tsare Babachir a ofishin EFCC


Korarren sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal zai cigaba da zama a ofishin hukumar yaƙi da yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC.

Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ita ta bayar da dama a tsare shi bayan da hukumar EFCC ta gurfanar da shi a gabanta ranar Talata.

Hukumar a ranar 30 ga watan Janairu ta shigar da tuhume-tuhume guda 10 a kansa.

Ana zargin Lawal da hada baki da wasu ma’aikatan kamfanin,Rolavision wanda mallakinsa ne wajen sayan kadarori.

Da aka karanta masa tuhume-tuhumen da ake masa Lawal ya musalta aikata wani laifi kana daga nan lauyansa ya nemi a bayar da belinsa.

Kotun ta yanke hukuncin a cigaba da tsare shi a ofishin EFCC har ya zuwa ranar Laraba lokacin da za ta saurari batun belinsa.

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya sallami Lawal daga bakin aikinsa bayan da wani kwamiti da ya kafa karkashin mataimakin shugaban kasa ,Yemi Osinbajo ya same shi da laifi wajen karkatar da kuɗaɗen yan gudun hijira dake yankin arewa maso gabas.


Like it? Share with your friends!

2
61 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like