Za A Canzawa Instagram Da WhatsApp Suna


Kanfanin manhajar sada zumuntar zamani ta Facebook ya sanar da aniyarsa ta sauyawa manhajojin sadarwar zamani na Instagram da WhatsApp suna nan bada jimawa ba.

Kamfanin na Facebook yace zai sauyawa kafafen sadarwar suna ne domin maido da kimarsu. Kazalika domin inganta ayyukansu da saukaka mu’amala a cikinsu.

Da yawan masu mu’amala da WhatsApp da Instagram na yi ne kawai basu San cewa kamfanin Facebook ne keda dandalin sadarwar biyu ba. Amma matakin da Facebook din ya dauka yanzu zai nuna karara mallakin waye.

Domin kuwa a yanzu sunan WhatsApp zai koma ne “WHATSAPP FROM FACEBOOK” a yayinda shi ma Instagram zai koma “INSTAGRAM FROM FACEBOOK” kenan kai tsaye Facebook ya sanya alamun mallaka a manhajojin biyu.


Like it? Share with your friends!

2
57 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like