Shugaban kasar Iraki Barham Salih yana cikin jerin mutane 50,000 da aka ware domin bin diddigin lambobin wayoyinsu, ciki har da Shugaban Faransa Emmanuel Macron a shari’ar da ake yi ta Pegasus kan zargin leken asiri.

Jaridar Washongton Post ta ruwaito cewa ba a samu damar tantance ko kamfanin Isra’ila mai leken asiri ta NSO da Pegasusu suna da alakar da ta shafi lambar wayar shaugaban Iraki ba ko wani yunkuri na yin haka.

Sakamakon binciken na cikin wani bangare na binciken kasa da kasa wanda ya shafi jaridar Washongton Post da wasu kungiyoyin yada labarai 16. Kakakin kungiyar NSO ya ki mayar da martani kan bukatar karin bayani dangane da batun daga jaridar Washington Post.