Zaɓen gwamnan Ekiti: za a tura jami’an tsaro 30,000


Hukumomin tsaro ciki har da rundunar ƴansandan Najeriya za su hada gwiwa wajen girke jami’an tsaro 30,000 da za su samar da tsaro a zaben gwamnan jihar Ekiti na ranar 14 ga watan Yuli.

Shirye-shirye sun yi nisa wajen karbar bakuncin babban sifetan ‘yansanda na kasa, Ibrahim Idris da zai kai ziyarar aiki jihar ta kwana daya.

Caleb Ikechukwu, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya fadawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Litinin a Ado-Ekiti cewa babban sifetan zai gana da dukkanin masu ruwa da tsaki a harkar zaɓen.

Mista Ikechukwu ya bayyana hukumomin samar da tsaro da suka hada da NSCDC,DSS, FRSC da kuma hukumar gidan yari ta kasa na daga cikin wadanda za su kasance a rundunar.

Ya yi karin haske cewa ba kamar yadda ake zato ba dukkanin jami’an da za a tura baza su ɗauki makami ba.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like