Yawan wadanda suka mutu ya kai 106 yayin da cutar coronavirus ta yadu zuwa kasashe 15


Kusan mutane 106 ne suka mutu aka kuma tabbatar da wasu su 4,515 sun kamu da cutar coronavirus a kasar China yayin da cutar ke cigaba da yaduwa a yankin Asiya da ma sauran ƙasashen duniya.

jumullar mutane 2,014 aka tabbatar sun kamu da cutar a ƙasashe 15 idan ka dauke kasar China.

An tabbatar da bullar cutar a kasashen Australia, Cambodia, Canada, France, Germany, Japan, Malaysia, Nepal, Singapore, South Korea, Sri Lanka, Taiwan, Thailand, US and Vietnam.

Kafar yada labarai ta CNN ta rawaito hukumomi a Hubei lardin kasar China da cutar ta faro na cewa an tabbatar da karin mutane 1300 da suka kamu da cutar hakan ya kawo jumullar mutanen dake dauke da cutar a yankin ya zuwa mutum 2700. Da yawa daga cikinsu suna asibiti inda sama da 125 suke cikin mawuyacin hali.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like