Makonni 45 bayan da Najeriya ta samu mutum na farko da ya kamu da cutar Korona a ranar 20 ga watan Fabrairu 2020 a yanzu yawan waɗanda suka kamu da cutar sun haura mutum dubu dari.

A bayanan da hukumar NCDC ta fitar na ranar 10 ga watan 1 ya nuna cewa an samu karin mutane 1024 da suka kamu da cutar a jihohi 16 da kuma birnin tarayya Abuja.

Jihar Lagos ita kaɗai na da yawan mutane fiye da rabin wadanda aka samu inda mutane 653 suka kamu da cutar sai jihar Plateau dake biye mata da mutane 63 sai kuma Benue mai mutane 48.

Mutane takwas aka tabbatar sun mutu a sanadiyar cutar inda hakan yasa kawo yanzu yawan wadanda suka mutu ya kai mutane 1358.

Jumullar mutane 100,087 aka tabbatar sun kamu da cutar a yayin da mutane 80,030 suka warke a fadin kasa baki daya.