Yawan mutanen da suka mutu sun zarta 30 a harin kunar bakin wake da aka kai Borno


Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Borno ta ce yawan mutanen da suka mutu a harin kunar bakin waken da mayakan Boko Haram suka kai garin Mandarari dake karamar hukumar Konduga ya haura mutane 30.

Bello Kachalla,daraktan dake lura da ayyukan ceto da kai dauki a hukumar ta SEMA ya ce mutane 47 da suka jikkata a harin na can suna karbar magani a asibiti.

Kachalla ya ce yan kunar bakin wake uku da suka kunshi mata biyu da namiji kwaya daya sun tayar da bam din dake jikinsu a wani wurin me sayar da shayi da kuma gidan kallo dake garin.

Ya ce mutane 17 ne suka mutu nan take a harin inda ya kara da cewa yawan mutanen da suka mutu ya karu zuwa 30 sakamakon rashin kayayyakin kula da lafiya.

Ya kara da cewa ma’aikatansu su gaza isa wurin da lamarin ya faru sakamakon rufe hanya da sojoji suka yi kana asibitin dake Konduga ba shi da kayan aikin da zai tunkari lamarin

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like