Yawan masu Coronavirus a Najeriya ya kai 51


Yawan mutanen da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ya kai 51 bayan da aka samu karin mutane biyar da suka kamu fa cutar.

Hukumar dake lura da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya NCDC ita ta sanar da haka cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.

Cibiyar ta ce uku daga cikin wadanda suka kamu da cutar sun dawo ne daga kasar waje yayin da biyu kuma suka yi cudanya da masu cutar.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like